Ku San Malamanku tare da Sheikh Aliyu Hammari Walama
An haife Sheikh Sheikh Aliyu Hammari Walama a garin Gombe da ke jihar Gombe a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Ya fara karatu a wajen kakansa wanda shi ne sarkin malaman Gombe, kafain daga baya a kai shi makarantar tsangaya ta Alaramma Yakubu Bara, in da ya sauke Qur'ani tare da karanta ƙananan littatafan fiqihu domin.
A ɓngeran karatun boko Shehin malamin ya yi karatun furamare da sakandire a Gombe inda ya zarce kwalejin kyo aikin shari'a da adinin musulunci inda ya samu shaidar karatu ta diploma.
Ya zarce jami'ar jihar Gombe inda ya samu digirinsa na farko a fannin ilimin tarihi, sannan ya tafi jami'ar Maiduguri inda ya sake samun wata digirin a fannin shari'a.
Ya samu horon aikin lauya a shekarar 2019 a makarantar horas da lauyoyi da ke Yola a jihar Adamawa.
Malamin ya koma Jami'ar Maiduguri inda yanzu haka yake digirinsa na biyu a fannin ilimin gado



