Ko rage yawan wutar lantarkin da Najeriya ta yi wa maƙwabtanta zai amfana mata?

..

Asalin hoton, GETTY IMAGES

Tun bayan da hukumar kula da samar da wutar lantarki ta Najeriya, NERC ta umarci kamfanonin da ke samar da wutar lantarki a ƙasar da su rage yawan wutar da suke bai wa ƙasashe masu maƙwabtaka, 'yan Najeriya ke tambayar ko hakan zai ƙara yawan wutar da suke samu?

Najeriya dai na bai wa ƙasashen Nijar da Togo da Benin wuta, wadda hukumar ta NERC ta ce ta yi yawa saboda saɓa yarjejeniyar kason da ya kamata a rinƙa ba su.

Hukumar ta NERC ta ce daga 1 ga watan Mayu har zuwa watan Oktoban 2024, kamfanonin masu samar da wuta za su rinƙa bai wa ƙasashen uku kaso shida cikin ɗari na yawan wutar da suke samarwa.

Yanzu dai abin tambaya shi ne ko ta yaya rage yawan wutar da ake bai wa maƙwabtan zai inganta wadda 'yan Najeriyar ke samu a cikin gida?

'Matakin inganta wuta a cikin gida ne'

Sharfuddeen Zubair Mahmoud, masani kan harkokin wutar lantarki a Najeriya ya ce matakin rage wutar ƙasashen uku zai taimaka wajen wadatar da 'yan ƙasa.

"An fi bai wa ƙasashen uku fiye da 'yan Najeriya saboda wata yarjejeniya da Najeriya ta shiga da ƙasashen.

Ko da an samu ragayya a wutar to sai ka ga za a ci gaba da bai wa su ƙasashen wutar da aka saba ba su amma mu a nan Najeriya mu ne abin zai shafa." In ji Sharfuddeen.

Ya ƙara da cewa "idan ka dubi tsarin sam babu adalci a ciki kasancewar ɗan ƙasa ba a iya biya masa buƙatarsa ba amma ana biyan ta wasu wato kenan mun zama inuwar giginya na nesa ka sha daɗi. Yanzu ai dole wutar da za a rage a bai wa masu saye kaga wuta za ta wadata a tsawon watannin shida masu zuwa"

Da kuma aka tambayi masanin kan ko kawo yanzu wutar ta inganta? Sai ya ce "gaskiya ba ni da alƙaluma kan hakan."

To sai dai wasu masu amfani da wutar lantarki da BBC ta zanta da su sun bayyana cewa tun bayan wannan sanarwar da hukumar ta NERC, sun fuskanci ƙarin sa'a'o'in da suke samun wuta a kullum.

"Gaskiya tun daga ranar Asabar na fuskanci a unguwarmu mun samu ƙarin wuta fiye da a baya. Amma dai ba zan iya alaƙanta ta da wannan sabon tsarin ba." In ji wani mazaunin birnin Kano.

To sai dai rahotanni sun nuna cewa tun bayan da hukumar mai kula da samar da wutar lantarki ta Najeriya, NERC ta bayar da umarnin, wuta a Najeriyar ta ƙaru daga megawatts 3,000 zuwa 4,700.

..

Asalin hoton, TCN

Me ya sa Najeriya ta rage wutar Togo, Nijar da Benin?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sharfudeen Zubair Mahmoud ya ce dalilin da ya sa Najeriya ta ɗauki wannan mataki na rage abin da ake bai wa ƙasashen Togo da Benin da jamhuriyar Nijar, shi ne ƙoƙarin gamsar da kwastomomi a cikin gida sakamakon cire tallafin wutar lantarki.

"An cire tallafi abin da ya janyo ƙarin ƙuɗn wuta ga mutanen da ke kan layin ajin A ko kuma Band A a Turance. To amma idan ka duba babu wutar kuma jama'a na biya. Kuma a doka idan aka yi mako guda ba tare da samun wuta ta awa 20 ba a kullum ta za a matsar da mutane daga ajin Band A zuwa Band B.

To ka ga dole ne a nemo inda wutar nan take a bai wa 'yan ƙasa domin gudun afkuwar wancan al'amari." In ji Sharfuddeen.

Dangane kuma na dalilin da ya sa hukumar kula da samar da wutar lantarki ta Najeriyar ta rage wutar na tsawon watanni shida wato daga watan Mayu zuwa watan Oktoba, Sharfuddeen ya ce

"Gaskiya ban san dalili ba amma ba zai rasa nasaba da yadda a wannan lokacin za ka ga kusan kowa yake buƙatar wutar lantarki saboda yanayin zafi.

Kenan watakila zuwa lokacin da suka ɗeba na watanni shida yanayin tsananin buƙatar ya wuce daga nan zai a sake yin duba kan yarjejeniyar." In ji masanin.

Ta yaya ragin zai shafi ƙasashen uku?

Rage yawan wutar da Najeriya ke bai wa ƙasashen masu maƙwabtaka ka iya shafar yadda ƙasashen ke gudanar da al'amuransu na yau da kullum musamman kamfanoni.

Misali fiye da kaso 70 na jamhuriyar Nijar ya kasance a cikin duhu lokacin da ƙungiyar tattalin arzikin ƙasashen Afirka ta Yamma, Ecowas ko Cedeao ta sanya wa jamhuriyar takunkumi, inda kuma Najeriya ta yanke wutar lantarki na wani tsawon lokaci.

Duk dai cewa sabon tsarin da hukumar NERC ta fitar zai bai wa ƙasashe kaso shida sannan kuma wasu daga cikinsu na ta ƙoƙarin gina dam-dam domin samar da wutar su ta ƙashin kansu, amma masana na cewa dole ne matakin ya shafe su.

"Lallai dole matakin ya shafi masana'antu da masu gidaje to amma ba za mu iya ƙayyade girman al'amarin ba." In ji Sharfuddeen Zubair Mahmoud..

Yarjejeniyar wuta tsakanin Najeriya da maƙwabta

..

Asalin hoton, Getty Images

Bayanai dai sun cewa a shekarun 1970s ne Najeriya ta rattaɓa hannu kan wata yarjejeniyar hana ƙasashe masu maƙwabtaka da ita da suka haɗa da jamhuriyar Nijar da Benin da Togo gina dam domin gudun katse ruwan kogin River Naija da ya ratsa ta ƙasashen.

A shekarar 2020 ma sai da gwamnatin shugaba Buhari ta sake sabunta yarjejeniyar wadda ta nemi ta kare tashoshin samar da wutar lantarki na Najeriya da ke amfani da ruwa da suka haɗa da Kainji da Shiroro da Jebba.

Wannan ne ya hana ƙasashen gina dam-dam bisa alƙawarin cewa Najeriyar za ta rinƙa ba su wuta su kuma su rinƙa biya.

To sai dai a lokuta daban-daban, Najeriyar ta sha kokawa dangane da irin maƙudan kuɗaɗen take cewa tana bin ƙasashen sakamakon rashin biyan kuɗn wuta na tsawon lokaci.

Ko a shekarar 2020 sai da ministan wutar lantarki Babaraji fashola ya ce Najeriya na bin ƙasashen guda uku tsabar kuɗi har fiye da dalar Amurka miliyan 64.

Da dama dai na ganin cewa lokaci ya yi da ya kamata a sake zama a duba wannan yarjejeniyar musamman a daidai lokacin da "mai doki ke neman komawa kutiri."