Zaɓen Amurka 2024: Yadda katangar tsakanin Amurka da Mexico take
Ɗaya daga cikin manufofin Donald Trump idan ya samu nasara a zaɓe mai zuwa shi ne gina takanga a tsakanin Amurka da Mexico domin daƙile kwararar ƴancirani.
A shekarar 2017 ce dai Donald Trump lokacin yana shugaban ƙasar Amurka ya ayyana ƙudurinsa na gina kantangar a kan iyakarsu da Mexico daga kudanci.
A lokacin ya bayyana cewa Amurka ce za ta ɗauki nauyin aikin gina katangar mai tsayin mil 2,000, amma daga baya Mexico ta mayar mata da kuɗinta, lamarin da ita Mexicon ta ce ba za ta amince ba.
Haka kuma kotun ƙolin Amurka ta amince masa yin amfani da kuɗi daga ma'aikatar tsaro ta Pentagon domin gina katangar.
A wancan lokacin, an ƙiyasta katangar za ta ci zunzurutun kuɗi dala biliyan biyu da miliyan ɗari biyar.
Ma'aikacin BBC Hausa, Haruna Ibrahim Kakangi ya ziyarci kan iyakar ƙasashen biyu.



