Burina na zama kamar Rahma Sadau - Sadi Baby
Burina na zama kamar Rahma Sadau - Sadi Baby
A wannan makon za mu kawo muku tattaunawa da tauraruwar fina-finan Kanyywood, Hudallah Tahir Jalalain ko kuma wadda aka fi sani da Sadi Baby wadda kuma ta yi rayuwarta tun daga haihuwa har zuwa girmanta a birnin Kano.
Matashiyar wadda ƴar asalin ƙasar Sudan ce ta ce ta shiga harkar fim ne domin ta samu tsani na zuwa wurin da take son zuwa a rayuwarta.
"Fim zai taimake ni wurin zama abin da nake son na zama. Ina son na zama mai faɗa a ji ko kuma ƴar jarida."
Ta ce yanzu ta fara daga fim ɗin Ɗaɗin Kowa amma burinta na da yawa da take son cimma ta hanyar fim.



