Boxing Day: Ranar ruwan kyauta
Wani ɓangare na ƙololuwar Bikin Kirsimeti ga al'ummar Kirista shi ne washe gari, ranar rabon kyautuka da kyautatawa da kuma nuna godiya kan duk wani abin alheri na abokan zaman tare.
"Boxing Day" - babbar rana ce ta faranta zukata da sanya annuri ga fuskokin 'yan'uwa da abokan arziƙi.
Ranar wadda ita ce ta farko bayan Kirsimeti - ta samo asali ne a lokacin mulkin Sarauniyar Ingila Victoria cikin shekarun 1800.
Ranar ba ta da wata alaƙa da wasan damben da ake gudanarwa a faɗin duniya.
Sunan ya samo asali ne sakamakon ƙunshe kyauta da masu hali ke yi a cikin akwati "box" kafin su bai wa mabuƙata.
Boxing Day a al'adance, ita ce ranar da bayi kan yi hutun aiki sannan su karɓi kyautuka na musamman daga iyayen gidansu, kamar yadda Rabaran Ezekiel Bulus na Cocin ECWA da ke Narayin jihar Kaduna ya tabbatar mana.
Haka kuma, a ranar ne su ma suke zuwa gida domin bai wa iyalansu akwatunan kyautar.
Saurari cikakkiyar hirar daga bakin Rabaran a bidiyon da ke sama.



