Dan jarida mai digiri biyu da ke sana’ar tuyar ƙosai a Maiduguri
Dan jarida mai digiri biyu da ke sana’ar tuyar ƙosai a Maiduguri
Sunday Williams Omega, wanda aka fi sani da Danladi Zulum yana sana’ar soya ƙosai a birnin Maiduguri da ke jihar Borno.
Sunday na da digiri biyu a fannin aikin jarida, kuma ya yi aiki a ma’aikatun jarida da dama ciki har da gidajen rediyo da jarida a fadin Najeriya.
Yanzu haka Sunday na soya ƙosai da yamma bayan ya tashi daga aikin ofis.
Ya ce abin da ya sa ya rungumi sana’ar ƙosai, shi ne yadda ya ga mahaifiyarsa ta dauki nauyin karatunsa shi da ‘yan uwansa har zuwa jami’a ta hanyar ƙosai.



