Yadda aka yi hawan sallah a Kano

Bayanan bidiyo, Latsa alamar da ke sama domin kallo
Yadda aka yi hawan sallah a Kano

Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi hawan sallah yau bisa al'ada bayan sakkowa daga sallar Idi.

A irin wannan lokacin ne dai mai martaba sarkin na Kano kan isar da sako ga talakawa da mahukunta.

A ranar Alhamis ne kuma za a yi hawan Daushe wanda ya fi kowanne girma da daukar hankalin jama'a na ciki da wajen jihar Kano.