Yadda aka yi bikin nuna shiga ta kamala a kasar Ghana
Yadda aka yi bikin nuna shiga ta kamala a kasar Ghana
A ko wace shekara al'umma na shirya wani kayataccen biki domin nuna irin shiga ta kamala da mutunci a kasar Ghana.
A wannan shekarar ma an gudanar da bikin a karshen mako wanda darururwan mutane suka halarta.
Wannan shi ne karo na uku da bikin ke gudana a Ghana. Mata da maza daga yankunan kasar daban-daban ne su ke zuwa domin shiga bikin.
Suna sanya tufafi mai kayatarwa irin na gargajiya da kuma sauran kayan ado na kawa domin nuna kwalliyarsu akan dandamali ga mahalarta bikin.



