'Yunwa ce ta kashe matata'
'Yunwa ce ta kashe matata'
Kimanin mutum 43,000 ne aka yi kiyasin sun mutu a Somaliya bara, saboda amfanin gona bai kai ba. Damuna ta yi gardama a sassa da dama, kamar yadda rahoton gwamnati da na Majalisar Ɗinkin Duniya suka nuna.
Waɗannan ne alƙaluma na farko daga yankin ƙusurwar Afirka game da mutanen da yunwa ta hallaka.
Ana da yaƙinin cewa rabin waɗanda yunwar ta kashe yara ne ƙanana.



