Abin da ya sa muka yi rashin nasara a hannun Ivory Coast - Zaidu Sanusi

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
Abin da ya sa muka yi rashin nasara a hannun Ivory Coast - Zaidu Sanusi

Ana ci gaba da nazari kan dalilin da ya sa ƴan wasan Super Eagles na Najeriya suka yi rashin nasara a hannun Ivory Coast a wasan ƙarshe na Gasar cin kofin ƙwallon ƙafa ta nahiyar Afirka.

Ɗan wasan baya na Najeriya ya bayyana wa BBC cewa yanayin wasa da kuma rashin sa'a ne manyan abubuwan da suka hana Najeriya yin nasara.

Ya kuma bayyana halin da suka tsinci kansu bayan rashin nasara a karawar tasu ta ƙarshe a gasar, wadda aka buga a ƙasar Ivory Coast.