APC ba su iya mulki ba - Atiku Abubakar

Bayanan bidiyo, Latsa sama don kallon wannan bidiyo
APC ba su iya mulki ba - Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya kuma jagoran adawa, Atiku Abubakar ya soki jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar, da cewa kwata-kwata ba su iya mulki ba.

Ɗan takarar jam'iyyar PDP a zaɓen 2023, ya kuma yi zargin cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta jefa Najeriya cikin masifa saboda yadda take aiwatar da manufofin shugabancinta.

Atiku Abubakar ya bayyana haka ne a wani ɓangare na zantawar da BBC ta yi da ƙusoshin 'yan siyasar Najeriya a kan cikar mulkin dimokraɗiyya shekara 25 kai tsaye ba tare da katsewa ba a ƙasar.

Lamarin dai wani babban abin tarihi ne ga Najeriya, wadda ta koma kan tafarkin dimokraɗiyya a jamhuriya ta huɗu a 1999.

Kamar sauran ƙasashen Afirka da dama, Nijeriya ta yi fama da mulkin sojoji tun bayan samun 'yancin kanta a 1960.

Mulkin dimokraɗiyya wanda ake kira da jamhuriya ta ɗaya, zamaninsu Sardaunan Sakkwato ya katse ne shekara shida bayan samun 'yanci, yayin da jamhuriya ta biyu ta katse bayan shekara huɗu da 'yan watanni.

Tattaunawar dai ta mayar da hankali ne wajen jin ko kwalliya ta biya kuɗin sabulu a tsawon shekara 25 ɗin nan na mulkin farar hula?

Atiku Abubakar dai ya ce a ganinsa kwalliya ta biya kuɗin sabulu duk da yake an samu ɗumbin ƙalubale ko tuntuɓe, waɗanda kuma mafi yawansu ya ɗora alhakinsu a kan jam'iyya mai mulki.

Editanmu, Aliyu Abdullahi Tanko ya dai ja hankalinsa da cewa a lokacin mulkin PDP ne aka fara samun rikicin Boko Haram. Ku kalli bidiyon don jin amsarsa!