Kauyen da al'ummarsa ke shan ruwa tare da dabbobinsu daga kogi ɗaya
Kauyen da al'ummarsa ke shan ruwa tare da dabbobinsu daga kogi ɗaya
Firdausi yarinya ce 'yar shekara tara wadda take da burin zama malamar makaranta a rayuwarta.
To amma kash! Matsalar rashin ruwan sha a ƙauyensu na Famfara da ke karamar hukumar Bebeji a jihar Kano ta sa da wuya ta iya cika wannan buri nata.
A kullum Firdausi ta kan yi tafiya mai nisa zuwa kogi domin ɗebo ruwan sha ga mahaifanta, inda take tona rami domin ruwan kogin ya ɓulɓulo ta samu ta ɗiba.
Wani abin takaici ma shi ne yadda dabbobin garin nasu ke amfani da kogin wajen kiwo.
Albarkacin makon ruwa na duniya, BBC ta nemi jin ta bakin hukumomin da abin ya shafa amma hakan bai samu ba.



