'Ci gaban da BBC Hausa Facebook ya kawo mana a cikin shekara 14'

'Ci gaban da BBC Hausa Facebook ya kawo mana a cikin shekara 14'

Yau ne, Shafin BBC Hausa a Facebook ya cika shekara 14 da buɗewa, kuma a tsawon wannan lokaci ɗumbin masu sauraronmu na al'ada sun koma masu bibiyar shirye-shiryenmu ba kawai a rediyo ba, har ma da sabbin hanyoyin gabatar da labarai da rahotanni kamar bidiyo da hotuna da kuma tsari irin na jarida.

Ɗaya daga cikin mutanen da fara bibiyar wannan shafi a dandalin sada zumunta, Zaidu Bala Ƙofa Sabuwa ya ce kafar ta kawo musu ci gaba wajen hulɗa da BBC Hausa.

Saɓanin a baya, lokacin da wasiƙa ke ɗaukar tsawon lokaci, ko saƙon imel wanda mutum ba shi da tabbacin isar sa, sharhi (kwamen) a dandalin Facebook nan take yake isa, kuma yana bayar da damar musayar ra'ayi tsakanin masu bibiya da kuma BBC Hausa.

Zaidu ya ce hakan ya bai wa masu bibiyar BBC Hausa ƙarin damar bayar da gudunmawa cikin shirye-shiryenmu da bayyana ra'ayoyi da kuma faɗar albarkacin bakinsu.

Zaidu Bala