Ecowas ba ta yi mana adalci ba – Firaministan Nijar

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
Ecowas ba ta yi mana adalci ba – Firaministan Nijar

Firaministan Nijar, Ali Lamine Zeine, ya zargi Ecowas da nuna rashin adalci a takunkumin da ta ƙaƙaba wa ƙasar bayan hamɓarar da gwamnatin farar hula ta Bazoum Mohamed.

Firaministan ya bayyana haka ne a hira ta musamman da ya yi da BBC.

"Ba a taɓa yi wa wata ƙasa rashin adalci irin wadda aka yi mana ba, takunkumin da aka saka na hana shigo da magunguna, abinci, da yanke wutar lantarki wa al'ummarmu bai dace ba," in ji Firaministan.

Sai dai ya ce suna ci gaba da tattaunawa da Ecowas ɗin domin ganin an janye waɗannan takunkuman.

Ya ce akwai sharuɗan da Ecowas ɗin ta gindaya musu kafin janye takunkumin.

"Na farko Ecowas sun ce sai mun buɗe kofar tattaunawa don samun sulhu wanda kuma mun cika shi saboda Janar Abdussalami da Sarkin Musulmi da kuma manyan malamai daga Najeriya sun zo nan Nijar mun tattauna.

"Na biyu sun buƙaci ganin tsohon shugaban ƙasa, mun ba su dama, sun same shi cikin koshin lafiya ba kamar yadda kafofin yaɗa labarai a Turai (suka bayyana ba)" in ji Lamine Zeine.

Ya kuma musanta batun cewa sojojin sun ce sai bayan shekara uku za su miƙa mulki ga gwamnatin farar hula.

"Shugaban ƙasa bai faɗi haka ba, cewa ya yi za a ɗauki lokacin da ba zai fi shekara uku ba, kuma abu ne da yake hannun ƴan Nijar. Akwai babban taron da za a yi wanda ƴan ƙasa za su bayar da ra'ayinsu nan ba da jimawa ba.

A ɗaya ɓangaren, ya ce ƙasar za ta iya magance matsalolin tsaron da take fuskanta duk da ficewar sojojin Faransar.