Mutanen da Zakkar fidda-kai ta wajaba a kansu
Malamai sun ce bisa nassi an fara Zakkar Fidda-kai ne bayan hijirar Annabi Muhammad SAW da shekara biyu, wato a shekarar da aka wajabta azumin Ramadan, saboda haka Sunna ce mai karfi da ke da nufin wanzar da zaman lafiya tsakanin al'ummar musulmai.
Mutanen da Zakkar fidda-kai ta hau kansu
Dangane kuma da wadanda Zakkar ta wajaba a kansu, Sheikh Halliru Maraya, malamin addinin Musulunci a Kaduna, ya ce zakkar fidda-kai wajibi ce ga duk wani Musulmi da ke da hali walau dai namiji ko mace, yaro ko babba.
"Idan mutum yana da wadata zai fitar a kansa ya kuma fitar wa da wadanda ke karkashinsa wato mutanen da yake ciyar da su.
Zakkar tana kan dukkan musulmin da yake ya wadatu, wadata ta bangaren abincin da za a ci da kuma wadata ta bangaren kudaden da zai iya bayarwa a sai abincin da su". In ji Sheikh Halliru.
Ga yaran da suke marayu ne ana iya fitar musu daga cikin dukiyarsu, wasu kuma irin kyautar da ake musu ko kuma wadanda iyayensu ke buɗe musu asusun banki, duk za a fidda zakar cikin kudinsu.
Idan 'ya'yan mutum maza sun balaga kuma lafiyarsu kalau to zakkarsu ta sauka daga kan mahaifansu. Amma idan ya ce zai ci gaba da fitar musu duk da haka, to babu laifi a Musulince.
Idan kuma mata ne 'ya'yan mutum ko sun balaga zai ci gaba da fitar musu har sai sun yi aure sun yi tarayya da mazajensu, a lokacin ne zakkar take sauka daga kan mahaifinsu."
Tasirin Zakkar fidda-kai a cikin al'umma
Sheikh Halliru Maraya ya lissafa wasu abubuwa guda uku da ya ce su ne kashin bayan fitar da zakkar kono a tsakanin Musulmi:
- Tabbatar da wadatar abinci tsakanin musulmai, ko wanne musulmi ya yi sallah da abincin da zai ci da iyalinsa.
- Ana amfani da Zakkar Fidda-kai wajen kankare zunuban da musulmi ya aikata cikin azumi, wadanda ba su ɓata masa azuminsa ba amma sun rage masa lada.
- Tana kara zumunci da soyayyar juna tsakanin musulamai.
Yadda ake fitar da Zakkar fidda-kai
Sheikh Halliru Maraya ya ce ana fitar da Zakkar da dukkan wani nau'in abinci da al'ummar da mutum ke rayuwa cikinta ke ci, musamman tsaka-tsakin abincin da aka fi ci, ko kuma abincin da suka fi ci gwargwadon hali.
"Idan wurin da mutum yake garin kwaki ake ci to shi ya kamata ya yi zakkar da shi, idan dabino suke ci da shi za su yi."
Ya kara da cewa an fi son abin da kake ci ka fitar da zakkar da shi, amma ba "wajibi ba ne don mutum yana cin shinkafa a gidansa ace sai ya yi zakkar da ita," in ji Sheikh Halliru.
Dangane da kuma da ma'aunin da ake bayarwa, Sheikh Halliru Maraya ya ce "mizanin Zakkar Fidda-kai shi ne Sa'i daya ga kowanne mutum.
Sa'i daya wato mudu hudu ko kuma kwatankwacin nauyin kilogiram biyu da rabi na shinkafa, shi ne abin da ake so a fitar wa kowanne mutum daya a matsayin Zakkar Fidda kai.
Amma duk abin da aka bayar kasa da haka sunan shi sadaka. Akan bayar da kudin da za su iya sayan abincin da zai yi kimar kilogiram biyu da rabi. Amma domin samun cikakken lada mutum sai ya ba da kudin a sai abincin a yi masa zakkar."
Lokacin da Zakkar fidda-kai ke zama sadaka
Sheikh Maraya ya ce "lokacin fara fitar da zakkar ya sha banban daga mazhaba zuwa mazhaba a musulunce.
A mazhabar Shafi'iyya da zarar an ga watan Ramadan ko a ranar 1 ga watan za a iya ba da ita.
Malikiyya da Hambaliyya suna ganin sai ya rage kwana daya ko biyu azumi ya kare sannan za a fara raba zakkar. Saboda daya daga cikin manufofinta shi ne musulmai su yi bikin sallah da abinci wadatacce a gidajensu."
Dangane kuma da wajabcin Zakkar ta Fidda-kai Malam Halliru Maraya ya ce "wajibcinta yana farawa ne daga lokacin da rana ta faɗi a azumin karshe na watan Ramadana.
Da an dawo daga sallar Idi to lokacin Zakkar Fidda-kai ya fita, komai aka ba da bayan nan daidai da sadaka yake. Wannan na cikin dalilan da yasa ake jinkirta Sallar Idi domin mutune su samu su fitar da zakkar kan lokaci ya kure.



