Ranar Rediyo ta Duniya
Ranar Rediyo ta Duniya
"Rediyo ne ya raba mana gardama kan mutuwar shugaban ƙasa."
13 ga watan Fabarairu ce ranar da Hukumar Raya Ilimi da Al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO ta ware a matsayin ranar rediyo.
UNESCO ta ware ranar 13 ga ko wane watan Fabrairu ne domin nuna muhimmancin da rediyon ke da shi a duniya.
Taken ranar na bana shi ne rediyo da zaman lafiya.
A ranar bukin ta shekarar 2023, mun tattauna da Babangida Tabako, wani mai sauraron rediyo wanda ya ce ya fara sauraron rediyo tun yana yaro.
A cewarsa akwai lokacin da rediyo ne ya raba masu gardama kan mutuwar tsohon shugaban Najeriya Janar Sani Abacha.



