'Mutuwa kawai muke jira'

h
    • Marubuci, Jean Mackenzie
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Seoul correspondent

Tun watanni masu yawa da suka wuce, BBC ta yi ta tattaunawa a asirce da wasu 'yan Koriya ta Arewa uku da ke zaune a ƙasar.

A karon farko sun fallasa irin bala'in da ke faruwa a can tun bayan da gwamnati ta rufe kan iyakokin ƙasar fiye da shekara daya da ta wuce.

Yunwa da matsananciyar takura, ga shi kuma babu damar kuɓuta. Mun canza sunayen mutanen don kare su.

Myong Suk na kan wayarta, tana kokarin gudanar da kasuwanci.

Ita ‘yar kasuwa ce mai dabara, tana sayar da magunguna a asirce ga masu tsananin bukata - don dai ta iya gudanar da rayuwarta.

An taɓa kama ta sau daya kuma da kyar ta iya bayar da cin hancin da ya fitar da ita daga gidan yari.

Ba za ta yarda a sake kama ta ba.

Amma a kowanne lokaci, ana iya ƙwanƙwasa mata kofa. Ba 'yan sanda kawai take tsoro ba, maƙwabtanta ne abin gudu.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Yanzu ba za ta iya amincewa da kowa ba. Amma ba haka yake a baya ba. Kasuwancin magungunan Myong Suk ya kasance mai bunƙasa.

Amma a ranar 27 ga watan Janairun 2020, Koriya ta Arewa ta rufe iyakarta a matsayin mataki kan ɓarkewar cutar korona, ba mutane kaɗai ta hana shiga da fita ba, har da abinci da sauran kayayyaki.

‘Yan ƙasar, waɗanda da ma an hana su fita, an sake killace su a garuruwa.

Ma'aikatan agaji da jami'an diflomasiyya sun tattara kayansu sun fice. Jami'an tsaro na shirin harbin duk wanda ya matso kan iyakar ƙasar.

Ƙasar da ta fi kaɗaici a duniya ta ƙara sake mayar da kanta saniyar ware daga sauran duniya.

A ƙarƙashin mulkin kama-karya na Kim Jong Un, an haramta wa ‘yan Koriya ta Arewa yin hulɗa da ƙasashen waje.

Da taimakon ƙungiyar Daily NK da ke gudanar da harkokin yaɗa labarai a cikin ƙasar, BBC ta samu damar tattaunawa da wasu mutane guda uku. Suna yunƙurin faɗa wa duniya irin bala'in da rufe iyakokin ƙasar ya yi wa rayuwarsu.

Sun fahimci cewa idan gwamnati ta gano suna magana da mu, za a iya kashe su.

Don kare su, za mu iya bayyana wasu daga cikin abubuwan da suka faɗa mana ne kawai, amma duk da haka abubuwan da suka fuskanta na ƙarin haske a kan halin da Koriya ta Arewa ke ciki.

Myong Suk
Myong Suk

Myong Suk ta faɗa mana "Halin rashin samun abinci da muke fuskanta bai taɓa yin muni irin wannan ba." Kamar yawancin mata a Koriya ta Arewa, ita ce ta fi samun kuɗi a cikin iyalinta. Takaitaccen albashin da maza ke samu a ayyukan gwamnatin da suke yi na tilas, ba wani amfani yake da shi ba, abin da ke tilasta wa matansu su ƙirƙiro hanyoyin da za su iya gudanar da rayuwarsu.

Kafin rufe kan iyakar, Myong Suk na shirya magungunan da ake bukata, gami da maganin riga-kafi, da za a yi jigilar su daga China, wanda za ta sayar a kasuwa ta cikin gida.

Takan bayar da cin hanci ga jami’an tsaron kan iyaka, wanda ke cinye fiye da rabin ribar da take samu, amma ta dauki hakan a matsayin wani ɓangare na gudanar da kasuwanci a irin wannan yanayin.

Ya ba ta damar yin rayuwa mai daɗi a garinsu da ke arewacin ƙasar, kusa da iyakar China.

Alhakin kula da iyalinta na jefa ta cikin damuwa, amma yanzu lamarin ya sake taɓarɓarewa. Ya zama kusan ba zai yiwu a samu kayan da za a sayar ba.

Wani lokaci da damuwar ta yi yawa, ta yi ƙoƙarin yin safarar magungunan da kanta, amma an kama ta, kuma yanzu ana sa mata ido. Ta yi ƙoƙarin sayar da magungunan da ake yi a Koriya ta Arewa a madadin haka, sai dai hakan ma yana da wahala a halin yanzu, don kuwa wannan na nufin yanzu tana samun rabin abin da take samu a baya.

Yanzu idan mijinta da 'ya'yanta suka tashi, ta shirya musu karin kumallon masara. Ba sa iya cin shinkafa yanzu. Yunwa ta ingiza maƙwabtanta har sun fara ƙwanƙwasa mata ƙofa suna neman abinci, sai dai dole ta sallame su.

"Muna rayuwa ne cikin wani mummunan hali," in ji ta.

Chan Ho

A wani gari da shi ma yake kan iyaka, Chan Ho, wani ma'aikacin gini mai taurin kai, yana cikin takaici.

"Ina so mutane su san cewa ina baƙin cikin haifa ta da aka yi a ƙasar nan," in ji shi.

.

Ya sake tashi da wuri don ya taimaki matarsa ​shirin zuwa kasuwa, kafin ya nufi wurin aikin gininsa. Ya ɗauki kayanta ya shirya mata rumfarta, yana sane da cewa sana'arta ce abin da ke kula da rayuwarsa.

Won kuɗin Koriya ta Arewa 4,000 da yake samu a rana - kwatankwacin dala 4 (£ 3) - bai isa ya sayi kilo ɗaya na shinkafa ba, kuma an daɗe rabonsa da samun abincin gwamnati.

Kasuwannin da akasarin ‘yan Koriya ta Arewa ke sayen abincinsu, yanzu sun kusa zama babu kowa, sannan farashin shinkafa da masara da kayan yaji sun yi tashin gwauron zabi.

Domin Koriya ta Arewa ba ta samar da isasshen abinci da za ta iya ciyar da al’ummarta, ta dogara ne kan shigo da kayayyaki daga kasashen waje. Da ta rufe iyakokin, gwamnati ta katse muhimman kayan abinci, da takin zamani da injinan da ake buƙata don noma.

Da farko Chan Ho ya ji tsoron zai mutu sanadin cutar korona, amma da lokaci ya ci gaba, ya fara tunanin cewa yunwa ce za ta kashe shi, musamman yayin da yake ganin waɗanda ke kusa da shi suna mutuwa.

Iyali na farko a ƙauyensu da suka faɗa cikin bala'in yunwa, uwa ce da ƴaƴanta.

Ta yi rashin lafiyar da ya hana ta yin aiki. 'Ya'yanta sun yi ƙoƙarin kula da ita har tsawon wani lokacin da za su iya, ta hanyar roƙon abinci, amma a ƙarshe su ukun duka suka mutu.

Bayan haka, sai wata uwa da aka yanke mata hukuncin aiki mai tsanani saboda ta karya dokar kulle.

Yunwa ta hallaka ta tare da ɗanta. A baya-bayan nan, an sako ɗaya daga cikin waɗanda ya sani daga aikin soja saboda rashin abinci mai gina jiki. Chan Ho ya tuna cewa fuskarsa ta fara kumbura.

A cikin mako guda ya rasu. “Ba zan iya yin barci ba idan na yi tunanin ’ya’yana, don su rayu har abada a cikin wannan mawuyacin halin,” in ji shi.

Ji Yeon

A nesa da su, a cikin kwatankwacin wadatar babban birnin Pyongyang, Ji Yeon ta hau jirgin karkashin kasa don yin aiki. A gajiye take, bayan ta shafe dare ba ta yi bacci ba.

Ji Yeon a gaban gidanta

Tana da ’ya’ya biyu da mijinta da ta ke tallafawa da kudaden da take samu a aikin da ta ke yi a kantin abinci.

Ta kasance tana dibar 'ya'yan itace da kayan lambu daga shagon don sayarwa a kasuwa, tare da sigarin da mijinta ya karba a matsayin cin hanci daga abokan aikinsa.

Za ta sayi shinkafa da kudin. Yanzu ana bincikar jakunkunanta sosai idan za ta fita, kuma cin hancin da mijinta ke samu ya daina shigowa.

Babu wanda ke iya bayar da wani abu yanzu.

''Yanzu sun hana kowa yin wani aiki na dabam'' in ji ta . Yanzu dai Ji Yeon ta ci gaba da wayancewa kamar ta ci abinci sau uku, alhali kuwa sau daya ta ci. Za ta jure yunwa. Gara hakan da mutane su san ita talaka ce.

Ta na tuna makon da aka tilasta mata cin puljuk - wani hade-hade na kayan lambu, itatuwa da ciyawa, da aka nika.. Abincin dai ya yi daidai da lokacin mafi muni a tarihin Koriya ta Arewa - mummunan farin da ta addabi kasar a shekarun 1990, wacce ta kashe mutane kusan miliyan uku.

"Muna tsira ta hanyar tunanin kwanaki 10 a gaba, sai kuma wasu 10, muna tunanin cewa ko da ni da mijina za mu yi fama da yunwa, akalla za mu ciyar da yaranmu," in ji Ji Yeon.

Cikin kwanakin nan ta yi kwana biyu babu abinci. "Na dauka zan mutu idan na kwanta bacci kuma ba zan farka da safe ba," in ji ta.

Duk da wahalhalun da take ciki, Ji Yeon na kokarin taimaka wa wadanda suka shiga hali mafi muni.

Mabarata sun kara yawa yanzu, ta tsaya ta duba wadanda suke kwance, amma yawanci sai ta ga sun mutu.

Wata rana ta kwankwasa kofar makwabtanta domin ta ba su ruwa, amma babu amsa.

Lokacin da hukumomi suka shiga ciki bayan kwanaki uku, sun gano cewa dukan iyalin sun mutu da yunwa.

Ta ce "bala'i ne." "Mutane ba su san yadda za su gudanar da rayuwa ba tare da samun kayayyaki daga kan iyaka ba.''

Kwanan nan ta ji labarin mutane suna kashe kansu a gida, yayin da wasu suka nufi a cikin tsaunuka don su samu wurin mutuwa.

Ta yi takaicin irin halin rashin tausayin da ya mamaye birnin.

"Ko da mutane sun mutu a makwabtan ku, tunanin kanku kawai kuke yi, rashin tausayi ne."

Hoton yan Koriya ta Arewa sanye da takunkumi suna jiran jirgin kasa ya wuce a birnin Phyongysong.

Asalin hoton, NK News

Bayanan hoto, Hoton yan Koriya ta Arewa sanye da takunkumi suna jiran jirgin kasa ya wuce a birnin Phyongysong. An dauki hoton ne a lokacin cutar korona

An shafe watanni ana ta yada jita-jitar cewa yunwa na ta kashe mutane, lamarin da ya sa ake fargabar cewa Koriya ta Arewa za ta sake fuskantar wani mummnan fari.

Masanin tattalin arziki Peter Ward, wanda ya yi nazari a kan Koriya ta Arewa, ya bayyana wadannan labarun a matsayin "abin damuwa sosai".

"Yana da kyau a ce kun ji labarin mutanen da yunwa ke kashewa, amma idan zahiri kun san mutanen da ke kusa da ku suna fama da yunwa, wannan yana nufin yanayin rashin abinci ya yi matukar tsanani - ya yi muni fiye da yadda mu ke tunani kuma ya fi muni tun lokacin farin da aka yi a karshen shekarun 1990," in ji shi

Farin da aka yi a Koriya ta Arewa ya kawo sauyi a cikin gajeren tarihin kasar, wanda ya haifar da tabarbarewar tsarin zamantakewar ta.

Gwamnati ta kasa ciyar da al'ummarta, ta ba su gutsuren 'yanci don yin abin da suke bukata don rayuwa.

Dubban mutane ne suka tsere daga kasar, suka sami mafaka a Koriya ta Kudu, ko Turai, ko Amurka.

A halin da ake ciki, kasuwanni masu zaman kansu sun bunkasa, yayin da mata suka fara sayar da komai daga waken soya, zuwa tufafi da na'urorin lantarki na kasar China.

Ya haifar da tattalin arzikin da ba na yau da kullun ba, kuma a hakan an samu 'yan Koriya ta Arewa wadanda suka koyi rayuwa ba tare da wani taimako daga gwamnati ba - ƴan jari hujja da ke bunkasa a cikin kasa mai tsattsauran ra'ayin tattalin arziki.

Hoton wasu yara masu fama da yunwa a lokacin bala’in yunwa na Koriya ta Arewa a shekarun 1990

Asalin hoton, NK News

Bayanan hoto, Hoton wasu yara masu fama da yunwa a lokacin bala’in yunwa na Koriya ta Arewa a shekarun 1990

Yayin da aka fara watsewa daga kasuwa, Myong Suk tana kirga yawan kudin da ta samu, ta damu cewa gwamnati za ta sa masu ido tare da wasu ra'ayin jari-hujja.

Barkewar korona, ta bai wa hukumomi uzuri ne kawai don kara matsa lamba kan rayuwar mutane.

"Hakika suna son murkushe masu fasa kwauri da hana mutane tserewa," in ji ta.

"Yanzu, idan ma kawai ka kusanci kogin zuwa kasar China, za a yi maka hukunci mai tsanani."

Chan Ho, ma'aikacin gine-gine, shi ma yana dab da kaiwa bango. Wannan shi ne lokaci mafi wahala da ya taba rayuwa a ciki.

Yunwar ta yi yawa, in ji shi, amma ba a sami irin wannan mugunyar takura da hukunta masu laifi ba.

"Idan mutane suna son tserewa, gwamnati ba za ta iya yin wani abu ba," in ji shi. "Yanzu, daga ka yi kuskure daya, ka na fuskantar kisa."

Kwanan nan dan abokinsa ya shaidi hukuncin kisa da dama da gwamnati ta yi. A kowane hukunci an kashe mutane uku zuwa hudu.

Laifinsu na kokarin tserewa ne. "Idan na rayu bisa ka'ida, tabbas zan mutu da yunwa, amma ta wurin kokarin tsira, ina tsoron a kama ni, a dauke ni mayaudari, a kuma kashe ni," in ji Chan Ho. "Mun makale a nan, muna jiran mutuwa."

Kafin a rufe iyakar, sama da masu tserewa 1,000 ne ke zuwa Koriya ta Kudu duk shekara, amma tun daga lokacin wasu tsiraru ne kawai aka san cewa sun gudu.

Hotunan tauraron dan adam da wata kungiya mai zaman kanta ta Human Rights Watch ta tantance, ya nuna cewa hukumomi sun shafe shekaru uku suna gina katangu da shinge da wuraren zaman masu gadi da dama don karfafa rufe iyakar, lamarin da ya sa ba a iya guduwa.

Hoton da tauraron dan’adam ya dauka

Yanzu ba karamin hadari ba ne ke tattare da kokarin tuntubar mutane a wajen kasar.

A baya, mazauna kusa da kan iyaka sun iya yin kiran waya a asirce zuwa kasashen waje ta yin amfani da kamfanoni sadarwa da ke China, da su ke amfani da wayoyin kasar China da aka shigo da su cikin kasar.

Yanzu, a duk wani taron al'umma, Chan Ho ya ce duk wanda ke da wayar kasar China, ana gaya masa ya mika kansa zuwa ga hukuma.

Kwanan nan an kama wani abokin Myong Suk yana magana da wani a China, kuma zai yi shekaru da dama a gidan yari.

Ta hanyar dakile fasa kwauri da kuma alakar mutane da kasashen waje, gwamnati na kwace wa ‘yan kasarta hanyoyin da za su iya neman abin kansu, in ji Hanna Song daga cibiyar kare hakkin dan Adam ta Koriya ta Arewa (NKDB).

"A lokacin da abinci ya riga ya yi karanci, tana da cikakkiyar masaniya game da barnar da wannan zai haifar," in ji ta.

Duk da haka wadannan tsauraran matakan ba za su iya hana cutar korona shigowa kasar ba.

A ranar 12 ga Mayu, 2022, kusan shekaru biyu da rabi bayan barkewar cutar, Koriya ta Arewa ta tabbatar da bullar cutar a karon farko. Da yake babu wata hanya ta gwada mutane, wadanda ke fama da zazzabi, a zahiri, an kulle su a cikin gidajensu ne na tsawon kwanaki 10.

An hana su da dukkan mutanen gidansu ko lekawa waje. Yayin da cutar ta cigaba da yaduwa, an kulle dukkan garuruwa da tituna, a wasu lokuta ma har tsawon sama da makonni biyu.

A Pyongyang, Ji Yeon ta ga yadda wasu makwabtanta da ba su da isasshen abinci, ake ajiye masu kayan lambu a kofar gidajensu kowace rana. Amma a gefen iyakar babu irin wannan taimakon.

Myong Suk ta firgita. Rayuwarta ta zama ta yau da kullum, ma'ana ba ta da komai na abinci a gidanta.

A haka ne ta karasa da sayar da magani a asirce, tana da yakinin cewa gwamma ta nemi kudi ko da za ta kamu da cutar da ta zauna yunwa ta kashe ta.

Chan Ho ya ce iyalai biyar na gab da mutuwa a lokacin da aka sake su daga kullen.

Sun tsira ne kawai ta hanyar fita a boye da dare don neman abinci. "Wadannan mutanen da ke cikin matsatsi kuma suka zauna a gida ba za su kai labari ba," in ji shi.

“Mutane sun yi ta kururuwa, suna cewa yunwa za ta kashe su, kuma a ‘yan kwanaki gwamnati ta saki wata shinkafar gaggawa daga cikin rumbunta,” inji shi.

Akwai rahotannin da ke cewa a wasu yankunan an dakatar da kullen da wuri lokacin da aka tabbatar da cewa mutane ba za su tsira ba.

Wadanda suka kamu da kwayar cutar ba za su iya dogara ga asibitocin kasar don yi musu magani ba. Kananan magunguna ma sun kare. Shawarar hukumar gwamnati ita ce a yi amfani da magungunan gargajiya don rage alamun cutan.

Lokacin da Ji Yeon da kanta ta yi rashin lafiya, ta kira abokanta don neman shawarwari. Sun bayar da shawarar ta sha ruwan zãfi da aka hada da koren albasa.

.

Mun gabatar da bincikenmu ga gwamnatin Koriya ta Arewa (DPRK).

Wakilin ofishin jakadancinta da ke Landan ya bayyana cewa: “Bayanan da kuka tattara ba gaskiya ba ne baki daya, domin sun samo asali ne daga kagaggun shedu daga dakarun da ke adawa da DPRK, a ko da yaushe DPRK tana bayar da fifiko ga jin dadin jama'a ko da a lokuta masu wahala, kuma tana bayar da matukar kula kan walwalar al'ummarta.

''Jin dadin jama'a shi ne babban abin da muka sa a gaba, ko da a cikin rashin jin dadi da kalubale."

BBC na son gode wa Lee Sang-Yong da tawagar Daily NK da suka taimaka mana wajen tattara wadannan bayanan.

Muna kuma gode wa Chung Seung-Yeon da tawagar NK News don taimaka mana wajen tabbatar da wasu abubuwan da muka gano, da kuma samar mana da hotunan da aka dauka a Koriya ta Arewa.