Mun ga murɗiya ta zahiri a zaɓen Edo - Ighodalo
Mun ga murɗiya ta zahiri a zaɓen Edo - Ighodalo
Ɗantakarar jam’iyyar PDP a zaɓen gwamnan jihar Edo na 2024 Asue Ighodalo ya ce zaɓen na ɗaya daga cikin zaɓuka mafiya muni a tarihin Najeriya.
A hirarsa da BBC, Ighodalo ya ce bai ji daɗin yadda zaɓen ya kasance ba wanda hukumar zaɓe ta INEC ta sanar da ɗan takarar APC Monday Okpebholo a matsayin wanda ya yi nasara.



