Albarkar da Yesu Almasihu ya kawo wa Duniya

Bayanan bidiyo,
Albarkar da Yesu Almasihu ya kawo wa Duniya

Al'ummar Kirista na gudanar da shagulgulan nuna murna da zagayowar ranar haihuwar Yesu Kiristi, don nuna godiya da girmama zuwan Almasihu.

FItaccen malamin addinin Kirista, kuma shugaban ƙungiyar Kiristoci ta ƙasa reshen jihar Kaduna, Rabaran Joseph John Hayab ya ce muhimman abubuwan da ake gudanarwa a ranar Kirismeti sun haɗar da addu'o'i da waƙoƙin yabon Allah da kuma tunawa koyarwar Yesu.

Ya ce ko da yake akwai saɓani game da ainihin ranar da aka haifi Almasihu, amma an zaɓi ranar 25 ga watan Disamba don bukukuwan Kirismeti saboda lokacin ya dace da buƙatar hakan.

A cewarsa, babban abin la'akari game da bikin Kirismeti ga al'ummar Kirista, shi ne saƙon da Yesu ya kawowa duniya.