...daga Bakin Mai Ita tare da Ummi Ƙarama
...daga Bakin Mai Ita tare da Ummi Ƙarama
A wannan mako cikin shirin ...daga Bakin Mai Ita muna gabatar muku Ummi Muhammad Sani wadda aka fi sani da Ummi Ƙarama ta cikin fim ɗin Labarina.
Ta shaida wa BBC cewa, ita haifaffiyar birnin Kano ce amma ta fara karatun firamare a garin Baga na jihar Borno, kafin ta koma Kano, inda ta kammala sakandirenta.
Jarumar ta ce ta taso ne cike da sha'awar fim, ko da yake ba ta taɓa tunanin za ta iya yin wannan sana'ar ba.



