Matar da ke gyaran burtsatse don samar wa mutanenta tsaftataccen ruwa

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
Matar da ke gyaran burtsatse don samar wa mutanenta tsaftataccen ruwa

Maryam Ibrahim, ɗaya daga cikin masu gyaran famfon burtsatse a arewa maso gabashin Najeriya ta gyara kimanin famfon burtsatse 200, kuma burinta shi ne ta gyara sama da 10,000.

Tana cikin mata masu ƙoƙarin kutsawa cikin sana’o’in da maza suka yi kaka-gida.

Tana ƙara wa mata kwarin gwiwa wajen ganin sun tashi tsaye domin bayar da gudunmawa wajen samar da tsaftataccen ruwa a yankinta.