Za mu kama gurbatattu - Tubabbun 'yan daban da suka koma 'yan sandan sa-kai

Bayanan bidiyo, Kano Constabulary Recruits
Za mu kama gurbatattu - Tubabbun 'yan daban da suka koma 'yan sandan sa-kai

'Yan sandan sa-kai ko kuma 'yan sandan sarauniya kamar yadda wasu ke kiransu sun bayyana kudurin yin aiki tare da rundunar 'yan sanda ta jihar Kano wajen yaki da aikata laifuka.

A ranar Talata ne, rundunar 'yan sandan jihar Kano ta kaddamar da sabbin 'yan sandan sa-kan su 50, wadanda tubabbun 'yan daba da suka ajiye makamai kuma suka rungumi zaman lafiya.

Kwamishinan 'yan sandan Kano, CP Mohammed Usaini Gumel ne ya bullo da tsarin, a karkashin shirin shigar da al'umma cikin ayyukan 'yan sanda.

Yayin kaddamar da matasan, wasu da muka zanta da su, sun yi alkawarin yaki da laifuka musamman na daba a fadin jihar. Ga bayanin da suka yi wa BBC a wannan bidiyo.