'Kauyen da aka yi wa ruwan wata daya a cikin awoyi takwas'
'Kauyen da aka yi wa ruwan wata daya a cikin awoyi takwas'
Mutane da dama sun bata sannan an tabbatar da mutuwar da dama bayan koguna biyar a tsakiyar Venezuela sun yi ambaliyar ruwa.
Ambaliyar ruwan ta lalata gidaje da dama a garin Las Tejerias da ke babban birnin kasar, Caracas.
Mataimakin shugaban kasar Venezuela Delcy Rodriguez ya ce an kwarara ruwan da ya kamata a yi a wata daya cikin awoyi takwas.



