Sai na duba inda za a samu ruwa kafin na fara aiki, in ji makaho mai haƙa rijiya
Sai na duba inda za a samu ruwa kafin na fara aiki, in ji makaho mai haƙa rijiya
“Kafin na haƙa rijiya sai na san inda za a samu ruwa” a cewar wani mai larurar rashin ido da ke aikin haƙa rijiya a jihar Bauchi da ke arewacin Najeriya.
Mallam Sulaiman Musa ya shaida wa BBC cewa ya kwashe sama da shekara 30 yana sana’ar haƙa rijiya bayan ya gamu da larurar tun yana da shekara 11 da haihuwa.
Ya ce aikin haƙa rijiya ya fitar da shi kunya a lokacin da ya fara wannan sana’a tun da ƙuruciyarsa.



