Kalli jariran Falasɗinawa da ake fargabar za su rasu idan lantarki ta katse a Gaza
Kalli jariran Falasɗinawa da ake fargabar za su rasu idan lantarki ta katse a Gaza
Likitoci a Gaza sun ce nan gaba kaɗan asibitocin da ke kula da jarirai bakwaini za su shiga wani mawuyacin hali sanadiyyar ƙarewar man fetur na janareto.
Hakan zai sanya kwalaben da ake saka jariran su daina aiki, wanda hakan zai jefa su cikin hatsari.
Isra’ila ta yanke wa yankin Gaza ruwa da abinci da man fetur tun bayan harin da Hamas ta kai wa Isra’ilara ranar 7 ga watan Oktoba.



