Matar da ke koya wa masu ciki rawa don naƙuda ta zo musu da sauƙi
Matar da ke koya wa masu ciki rawa don naƙuda ta zo musu da sauƙi
Ku latsa hoton da ke sama don kallon biidyon:
Wata ungozoma ta samar da wata cibiyar taimakon masu juna biyu a Ivory Coast bayan da a gabanta wata rana wata mai ciki ta rasu a wajen haihuwa.
Tana wayar wa da mata kai da yadda za su motsa jiki har ta hanyar rawa.
Kashi biyu bisa uku na mace-macen da ake samu wajen haihuwa na faruwa ne a yankin kudu da hamadar sahara, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.
Yawancin matsalolin da ke jawo hakan ana iya kare faruwarsu.
Wakilin BBC Late Lawson ya ziyarci cibiyar wacce ke ƙoƙarin taimaka wa mata su haihu lami lafiya.



