Hakkokin dan adam guda biyar da ya kamata ku sani
Hakkokin dan adam guda biyar da ya kamata ku sani
Yau ce ranar ‘Yancin Dan Adam ta duniya wadda Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin nusar da al’ummar duniya dangane da hakkokinsu.
Tun dai a shekarar 1948 ne Majalisar ta Dinkin Duniya ta fitar da wani kundi da ke dauke da wadannan jerin ‘yancin ko kuma hakkoki.
Hajiya Amina Abubakar shugabar kungiyar FlexiSAF Foundation ta yi karin bayani kan wasu daga cikin manyan hakkokin na dan adam.



