Daga Bakin Mai Ita tare da Erm Boii

Bayanan bidiyo,
Daga Bakin Mai Ita tare da Erm Boii

Usman Yahaya Shu'aibu wanda aka fi sani da Erm Boii mawaƙin Hausa ne da ke yin salon Afrobeat na gambara.

An haife shi ne a jihar Kano inda ya yi makarantar firamare kafin ya tafi jihar Jigawa domin yin sakandare kuma yana shirye-shiryen shiga jami'a.

Erm Boii ya ce yana da burin fara waƙa ne tun yana firamare tare da abokansa amma a sakandare ya fara rerawa.

Sai dai ya ce ba lallai ne ya dogara da waƙa dindindin ba kasancewar mutanen gida (wato manya) ba su gamsu da lamarin ba.

Mawaƙin ya ce gwanayensa a waƙa su ne Auta Waziri da Hamisu Breaker da Dj Ab kuma yana da waƙa tare da Autan.

Cikin nasarorin da ya samu akwai samun damar zuwa jihohi 10 a Najeriya domin rera waƙa, kamar yadda ya bayyana wa BBC.