Abin da za ku yi ku ci ribar yawan al'ummar duniya
Abin da za ku yi ku ci ribar yawan al'ummar duniya
A wani ɓangare na Ranar Yawan Al'umma ta Duniya, mun yi nazari kan gudunmawar da kowa zai iya bayarwa don ganin yawanmu a duniya ya zama mai amfani da kyautata rayuwa.
Akan tuna da ranar ne a duk 11 ga watan Yuli, kamar yadda Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ta ware.
Zuwa yanzu, MDD ta yi ƙiyasin mutanen duniya sun kai biliyan 8,120,886,000.



