'Muna neman ƙarin masu zuba jarin da za su zaƙulo arziƙin jihar Nasarawa'
'Muna neman ƙarin masu zuba jarin da za su zaƙulo arziƙin jihar Nasarawa'
Gwamnatin jihar Nasarawa ta bayyana shirinta na baje-kolin bayanai kan albarkatun ƙasa da damammakin da Allah ya hore mata, ga masu zuba jari da masu buƙatar kafa kamfanoni da nufin zaƙulo arziƙin ma'adanai da na noma.
Ta ce za ta yi hakan ne a wani taro kan harkokin zuba jari da za ta buɗe a ranar Laraba 15 ga watan Mayun 2024.
Taken taron dai shi ne: “Taron zuba jari a jihar Nasarawa na 2024; farfaɗo da muradin kafa masana’antu”, da nufin bunƙasa samar da kuɗin shiga da samar da ayyuka.
Albarkatun noma da haƙar ma’adanai da kuma man fetur da iskar gas ne dai, ta ce za a fi mayar da hankali kansu.
Gwamnan Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule ya yi mana ƙarin bayani game da wannan taro a cikin wannan bidiyo na sama.



