Muhimman abubuwan da suka faru a shekarar 2022
Muhimman abubuwan da suka faru a shekarar 2022
2022 na cikin shekarun da ba za a manta da su ba a tarihin dan adam musamman saboda kalubalen da aka rika fuskanta.
Abubuwa da dama sun faru a shekarar wadanda suka hada da mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine da tsadar rayuwa da ambaliyar ruwa da zanga-zangar kin jinin gwamnatoci da sauye-sauyen gwamnati a wasu kasashen duniya.
Haka kuma a shekarar ne Sarauniya Elizabeth II, basarakiya mafi dadewa a karagamar mulkin Biraniya ta rasu bayan ta shafe shekara 70 a kan mulki.



