Sergio Reguilon zai haɗe da Messi a Inter Miami, Arsenal ta kafe kan Yildiz

Asalin hoton, Getty Images
Tsohon dan wasan baya na Tottenham da Manchester United Sergio Reguilon yana tattaunawa kan komawarsa Inter Miami don hadewa da Lionel Messi a gasar (MLS) bayan kwantiraginsa da Spurs ya kare a bazara. (Mail)
Chelsea ba za ta yi yunkurin dauko dan wasan bayan Crystal Palace Marc Guehi, mai shekara 25 ba, duk da cewa dan wasan na Ingila zai bar kungiyar a kyauta a bazara mai zuwa. (Express)
Chelsea dai tana sha'awar sayen dan wasan gaban Bournemouth Antoine Semenyo kuma tana son biyan kusan fam miliyan 78 kan dan wasan Ghana mai shekaru 25. (Fichajes)
Juventus ta ki amincewa da tayin kusan fam miliyan 58 daga Chelsea kan dan wasan gaban Turkiyya Kenan Yildiz mai shekaru 20. (TuttoJuve)
Har ila yau Arsenal ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen zawarcin Yildiz inda ta aika da wakilai domin kallonsa a wasan da Juventus ta buga da AC Milan a gasar Seria A ranar Lahadi. (Tuttosport)
Dan wasan gaban Manchester United Joshua Zirkzee, mai shekara 24, zai yi tunanin ci gaba da zama a gasar Premier idan ya bar Old Trafford, inda Everton da West Ham za su iya nemansa. (Talk)
James Ward-Prowse, mai shekara 30, yana shirin barin West Ham na dindindin a lokacin bazara, inda dan wasan tsakiyar na Ingila ya rasa damar taka leda tun da Nuno Espirito Santo ya karbi ragamar kungiyar. (FootballInsider)
Dan wasan bayan Uruguay Ronald Araujo ya ki amincewa da damar barin Barcelona a bazara, dan wasan mai shekaru 26 ya shaidawa Chelsea, da Liverpool, da Tottenham da Juventus cewa yana son ci gaba da zama a kulob dinsa. (Sports Espanya)
Amma Barcelona na iya siyar da Araujo a watan Janairu, bayan da ta sanya masa farashin kusan fam miliyan 35 don siyan mai tsaron baya. (Fichajes)
West Ham na sha'awar daukar dan wasan gaba na Real Madrid, Endrick a matsayin aro, amma za ta fuskanci hamayya daga Valencia da Real Sociedad kan sayen dan wasan na Brazil mai shekara 19 a watan Janairu. (Fichajes)
Arsenal na fatan za ta amince da sabuwar yarjejeniya da Bukayo Saka, mai shekara 24, a lokacin hutun kasa da kasa domin ci gaba da rike dan wasan na Ingila na dogon lokaci. (TBR Football)
Liverpool na ci gaba da tattaunawa da Ibrahima Konate, mai shekara 26, domin neman tsawaita kwantiraginsa, yayin da Real Madrid ke zawarcin dan wasan na Faransa. (FootballInsider)










