Yadda makiyaya ke cajin waya da hasken rana a wurin kiwo

Bayanan bidiyo, Latsa alamar da ke sama domin kallo
Yadda makiyaya ke cajin waya da hasken rana a wurin kiwo

Amfani da hasken rana a matsayin makamashi na daɗa samun karɓuwa hatta a wurare masu nisa, inda mazauna irin waɗannan wurare, ba su da hanyar samun lantarki cikin sauƙi.

Irin wannan makamashi mai tsafta na ci gaba da zama hanyoyin sauƙaƙa rayuwa.

Wani matashin makiyayi a Dajin Wawa-Zange na jihar Gombe, Muhammad Badamasi ya ce hasken rana ya kawo musu sauƙi, inda suke cajin wayoyinsu a wurin kiwo maimakon su dogara da kai cajin waya a wuraren da ake da lantarki.

Ya ce wayar sadarwar ta zama muhimmiyar hanya da yake sadarwa tsakaninsa da abokai da ƴan’uwa musamman idan wani al’amari ya taso don haka ba ya son rabuwa da waya a kowanne lokaci.