Ku San Malamanku Tare Da Malam Lawal Jibril Abdullahi
Shirin Ku San Malamanku na wannan makon ya tattauna ne da Malam Lawal Jibril Abdullahi
An haifi malamin ne a anguwar Gwange da ke birnin Maiduguri na jihar Borno.
Ya ce mahaifinsa ya rasu lokacin da yake da shekara huɗu a duniya, inda ya koma gidan kakansa mai suna Gwani Shettima.
Ya fara karatunsa na allo a makarantar Malam Audu da ke garin Bama, daga baya ya zarce zuwa Konduga wajen makarantar Malam Umar domin ci gaba da karatu.
Ya ce ya yi karatu a wajen malamai da dama.
Ya ce ya fi ƙwarewa kan fannin hadisi da fiqihu.
Ya ƙara da cewa mutane sun fi yi masa tambayoyi kan ɓangaren tsarki da alwala da sallah da aure da kuma rabon gado.
Ya ce suratul-Baqarah na cikin surori da ya fi jin daɗin karantawa.
Ya kuma ce yana da mata ɗaya da ƴaƴa 13.



