'Yadda na shahara wurin daukar hoto a arewacin Najeriya'

Bayanan bidiyo, Sani Maikatanga: Yadda na shahara a daukar hoto a arewacin Najeriya
'Yadda na shahara wurin daukar hoto a arewacin Najeriya'

Danna hoton da ke sama domin kallon wannan bidiyo

A 'yan kwanakin nan daya daga masu daukan hoto mafi shahara a arewacin Najeriya Sani Maikatanga ya lashe wata gasar masu daukar hoto ta Afirka.

A cikin wannan bidiyo, Sani Muhammad Maikatanga ya bayyana irin nasarorin da ya samu a sana'arsa ta daukar hoto, wacce ya fara shekaru 30 da suka gabata.

Ya ce daya daga abin da ya fi so a sana'arsa shi ne tallata al'adun arewacin Najeriya ga duniya, musamman bukukuwan al'ada.

Bidiyo da tacewa: Yusuf Ibrahim Yakasai