'Na shafe shekara 30 ina aikin gyaran titi kyauta a Najeriya'
'Na shafe shekara 30 ina aikin gyaran titi kyauta a Najeriya'
Daniel Dabo yana aikin gyaran titi na ne sa-kai a Abuja da Nasarawa tun shekarun 1900 domin sauƙaƙa wa masu ababen hawa yi tafiya.
Masu tafiya a kan titi sun bayyana cewa Daniel mutum mai ƙwazo, wanda yake aikin gyaran titi a kowane yanayi, ko da a cikin ruwan sama ne ko zafin rana.
"Idan na ga hanya ta lalace, ina gyarawa ba tare da an faɗa min ba"



