Ƙasashen Afirka 10 da suka fi girman kasafin kuɗi a 2025

A makon da ya gabata ne wasu ƙasashen Afirka uku suka gabatar tare da amince da kasafin kuɗinsu na shekarar da muke ciki, a wani mataki na bunƙasa tatattalin arzikin ƙasashen.
Ƙasashen Kenya da Tanzaniya da kuma Uganda sun gabatar da kasafin kuɗin da ya mayar hankali kan zaɓuka da tattalin arzikin ƙasashen.
A kowace shekara ƙasashen Afirka kan ƙara yawan kasafin kuɗaɗensu, wataƙila sakamakon raguwar darajar kuɗaɗen ƙasashen.
Alal misali Najeriya - wadda ta fi yawan al'umma a nahiyar Afirka - kasafin kuɗin ƙasar na bana ya zarta na shekarar da ta gabata da kusan rabi.
Haka ita ma Kenya kasafin kuɗinta na bana ya zarta na Tanzaniya da Uganda idan aka haɗa su wuri guda.
Me kasafin kuɗaɗen Afirka ya fi mayar da hankali?

Asalin hoton, Getty Images
Galibi kasafin kuɗin ƙasahen Afirka kan mayar da hankali wajen cimmma muradunsu na tattalin arziki da ci gaba.
Kasafin kuɗin ƙasashen Afirka na 2025 ma ƙunshe da muradun ci gaba da bunƙasar abubuwan more rayuwa da kuma ingantuwar al'amuran yau da kullum a ƙasashen.
Ƙunshin kasafin kuɗin ƙasashen Afirka na 2025 ya ware gagarumin kaso a fannin inganta abubuwan more rayuwa da ayyukan kyautata rayuwar al'umma da kuma bunƙasa tattalin arzikin ƙasashen.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Kowace shekara ƙasashen Afirka na ware maƙudan kuɗaɗe a kasafin kuɗaɗensu.
A wannan maƙala mun zaƙulo kuku ƙasashen Afirka 10 da suka fi girman kasafin kuɗi, kuma mun yi ƙiyasin da dala domin samun sauƙin lissafi.
1. Afirka ta Kudu - (Dala biliyan 141.4)
Ƙasar Afirka ta Kudu ce kan gaba wajen ware maƙudan kuɗaɗe a kasafin kuɗi a Afirka a 2025.
A wannan shekara ƙasar ta ware dala biliyan 141.4 a matsayin kasafin kuɗiinta.
Kasafin kuɗin ya fifita fannin abubuwan more rayuwa da ayyukan bunƙasa rauyuwar jama'a da ci gaban tattalin arziki.
2. Algeria- (Dala biliyan 126)
Ƙasar Algeria ce ke matsayi na biyu a yawan kasafin kudi a nahiyar Afirka a 2025.
Ƙasar - wadda ke arewacin Afirka - ta ware dala biliyan 126 a kasafin kudinta, inda tafifita fannnonin makamashi da tsaro.
3. Masar- (Dala biliyan 91)
Masar ce ta uku cikin jerin, mai adadin kuɗi har dala biliyan 91, inda ta ware kaso mai yawa zuwa fannonin ilimi da lafiya da ayyukan da za su amfani jama'a.
4. Morocco- (Dala biliyan 73)
Ƙasar Morocco - da ita ma ke yankin arewacin Afirka ta kasance a mataki na huɗu.
Morocco ta ware dala biliyan 73 a kasafin kudinta na shekarar 2025.
5. Angola - (Dala biliyan 37.847)
Angola - arzikin man fetur - ce a matsayi na biyar cikin jerin ƙasashen Afirka da suka fi ƙarfin kasafin kuɗi.
Ƙasar - wadda ke yankin kudancin Afirka - ware dala biliyan 37.847 domin kasafin kudinta na shekarar da muke ciki.

Asalin hoton, Getty Images
6. Nigeria - (Dala biliyan 36.7)
Najeriya - babbar yaya a Afirka - ce a matsayi na shida.
Ƙasar - wadda ta fi kowace ƙasa a Afirka yawan al'umma - ta ware dala biliyan 36.7 a kasafin kudinta na 2025.
Shugaban ƙasar Bola Tinubu ya ce ƙasar ta shirya kasafin kudin ne da nufin kawo gagarumin sauyi a tattalin arzikin ƙasar.
7. Kenya - (Dala biliyan 32.65)
Ƙasar Kenya da ke gabashin Afirka na da girman kasafin kuɗin da ya kai dala biliyan 32.65.
Kasafin kuɗin ƙasar ya fifita ɓangarorin ilimi da kiwon lafiya da ci gaban tattalin arziki.
8. Libya - (Dala biliyan 26)
Duk da kasancewarta cikin rikicin siyasa da fama da ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya, Libya ta kasance cikin ƙasashen Afirka 10 da suka fi girman tattalin arziki.
ƙasar - da ke arewacin Afirka - ta ware dala biliyan 26 a kasafin kudinta na 2025.
9. Ivory Coast - (Dala biliyan 25.22)
10. Tunisia - (Dala biliyan 25.16)
Ƙasashen Afirka ta Tunisiya ne cikon na tara da 10 a jerin lissafin, inda suka da yawan kasafin kudin da ya kai dala biliyan 25.22 da dala biliyan 25.16.
Bayanai daga mujallar ''Business Insider Africa''.











