Dan kishin kasar da ke zagaya Najeriya don mutane su mallaki katin zabe

Bayanan bidiyo, Dan kishin kasar da ke zagaya Najeriya don mutane su mallaki katin zabe
Dan kishin kasar da ke zagaya Najeriya don mutane su mallaki katin zabe

Danna hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Wani dan kishin kasar Najeriya Abba Adam wanda akafi sani da E Racket a kafafen sada zumunta ya lashi takwabin zagaya dukkan jihohin kasar domin fadakar da mutane muhimmancin mallakar katin zabe.

Abba ya ce ya fara fafutukar ganin mutane sun yanki katin zabe ne tun lokacin da Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta Kasa INEC ta yi korafin rashin masu yankar katin yadda ya kamata.

E Racket ya kuma ce kishin kasa ce ta sa ya ke yawon fadakar da mutane alfanun mallakar katin na zabe.

"Ba zancen zaben PDP ko APC ko kuma sauran jam'iyyu ba ne, abu mafi muhimmanci shi ne mallakar katin zabe" a cewarsa.

Ya zuwa yanzu, E Racket ya zagaye jihohi da dama a Najeriya kuma ya ce burinsa shi ne ya kammala shiga duk jihohin kasar.

Malamin ya kara da cewa magoya bayansa a kafafen sada zumunta ne ke bashi kwarin gwiwa wajen ci gaba da aikin da ya soma.

INEC dai ta ce a ranar 31 ga watan Yulin 2022 ne za ta rufe yin katin zabe.