'Zan farfaɗo da masana'antu domin samar wa matasa aiki a Yobe'
'Zan farfaɗo da masana'antu domin samar wa matasa aiki a Yobe'
A jerin tattaunawa da BBC ke yi da ƴan takara gabanin zaɓen gwamnonin jihohin Najeriya na 2023, BBC ta yi hira da ɗan takarar gwamnan jihar Yobe ƙarƙashin jam'iyyar ADC.
A tattaunawar, Abdullahi Muhammad Taliyo ya ce matasa ne suka ƙarfafa masa gwiwar fitowa ya nemi takara ganin yadda suka waye a ƙoƙarin da suke na samar da mutum na gari da zai jagorance su.
Game da manufofinsa idan aka zaɓe shi, Abdullahi Taliyo ya ce zai mayar da hankali wajen bunƙasa ilimi da inganta noma da kiwon lafiya.



