Kocin Benin Gernot Rohr na neman a hukunta Libya kan 'wahalar' da suka sha

Kocin Benin Gernot Rohr sanye da jan riga

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Gernot Rohr ya horas da Gabon, da Nijar, da Burkina Faso, da Najeriya, sai kuma Benin a yanzu
    • Marubuci, Oluwashina Okeleji
    • Marubuci, Ian Williams
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport Africa
  • Lokacin karatu: Minti 2

Tsohon kocin tawagar ƙwallon ƙafa ta Najeriya, Gernot Rohr - wanda ke jagorantar tawagar Benin a yanzu - na neman a hukunta ƙasar Libya bayan an "wahalar" da tawagarsa a birnin Tripoli.

Kocin mai shekara 71 na magana ne game da abin da ya ce magoya baya da jami;'an tsaron Libya sun aikata musu yayin wasan neman gurbin shiga gasar Kofin Ƙasashen Afirka wato Afcon 2025 a watan Nuwamba.

Ɗan ƙasar Jamus ɗin ya ce sai da ya nemi a duba shi a cikin motar tawagarsa bayan an jefe shi da sanda, yayin da sauran ma'aikatan tawagar aka tsare su a ɗakinsu bayan tashi daga wasan.

Libya na sa ran samun nasara ne a wasan don ta samu gurbi, amma sakamako 0-0 da aka tashi ya sa Benin ta ƙare a mataki na biyu a ƙasan Najeriya da ke Rukunin D don buga gasar da za a yi a Morocco.

Rohr wanda ƙwararre ne a harkar ƙwallon Afirka, ya horas da tawaga biyar a nahiyar har da Najeriya. Ya ce abin da ya faru shi ne mafi muni da ya taɓa gani a ƙwallon Afirka.

"Abin da ya faru a Libya abin tashin hankali ne," kamar yadda ya faɗa wa BBC Sprot Africa.

"Ban taɓa ganin irin wannan yanayin na Tripoli ba. Halayyar magoya baya, da yadda jami'an tsaro suka kawo mana hari. Ka yi hasashen yadda za a kulle mutum a ɗakin saka kaya. An ƙuntata mana.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Abu ne mai haɗari a dinga buga ƙwallon ƙasa da ƙasa a ƙasar da babu zaman lafiya a siyasance, babu tsaro, kuma hakan zai iya jawo ta'annati cikin sauƙi."

Kocin ya ƙara da cewa bai kamata a jira sai wani bala'i ya faru ba kafin a ɗauki mataki.

"Saboda haka ina fatan Caf (hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka) za ta yi abin da ya dace domin kare tawagogi nan gaba da za su je wasa Libya."

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Libya LFF ta ƙi yarda ta yi magana, amma wani jami'in hukumar ya faɗa wa BBC cewa ƙasar "na da kwanciyar hankali".

BBC ta tuntuɓi Caf amma zuwa lokacin haɗa wannan rahoton ba ta ce komai ba.

Fatan tawagar Libya da ake wa laƙabi da Mediterranean Knights ya ƙare ne bayan Caf ta bai wa Najeriya maki uku sakamakon soke wasan da ya kamata su buga a ƙasar a watan Oktoba.

Tawagar Super Eagles ta Najeriya ta ƙaurace wa wasan bayan an sauya wa jirginsu wurin sauka sannan aka bar su yashe a filin jirgi na tsawon lokaci.

A lokacin, mai magana da yawun Super Eagles, Promise Efoghe, ya ce babu wani jami'in LFF da ya je domin ya yi musu bayanin abin da ke faruwa, kuma ya bayyana lamarin da cewa "kamar suna cikin gidan yari ne" a filin jirgin.