Matan da suka maƙale a Oman cikin ƙangin bauta
Matan da suka maƙale a Oman cikin ƙangin bauta
Akwai mata ƴan ci-rani masu aikatau kimanin miliyan biyu a ƙasashen yankin Gulf, waɗanda wasu mutane masu zaman kansu ne ke sarrafa su yadda suka ga dama.
Shirin BBC Africa Eye ya binciki yadda ake safarar mata ƴan ƙasar Malawi, ake jefa su cikin ƙangin bauta da cin zarafi a Oman.
Haka nan rahoton ya bibiyu wasu mata da ke aiki tare a tsakanin nahiyoyi uku wajen yaƙi da wannan ɗabi’a tare da ƙoƙarin mayar da matan gida duk da ƙalubalen da suke fuskanta.



