Gwarzuwar Hikayata: 'Sirrin nasarar da na samu a gasar ta bana'
Gwarzuwar Hikayata: 'Sirrin nasarar da na samu a gasar ta bana'
Gwarzuwar gasar Hikayata ta 2024 Hajara Ahmad Hussain ta ce bai wuce mako biyu ba kafin rufe shiga gasar lokacin da fara shirin rubuta nata labarin.
A wannan bidiyon na sama, ta bayyana yadda ta samo jigon labarin Amon 'Yanci, wanda ya lashe gasar tare da samun kyautar naira miliyan ɗaya.
Hikayata gasa ce ta ƙagaggu kuma gajerun labarai cikin harshen Hausa da BBC Hausa ke shirya wa mata zalla duk shekara, kuma wannan ne karo na tara.



