Na isar da ƙorafin matasa ga shugaba Tinubu - Abbas

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
Na isar da ƙorafin matasa ga shugaba Tinubu - Abbas

Shugaban Majalisar wakilan Najeriya, Tajuddeen Abbas ya shawarci al'ummar ƙasar su kwantar da hankulansu tare da dakatar da zanga-zanga kasancewar shugabannin na tattaunawa kan matsalar da ke addabar ƙasar.

Tajuddeen ya yi wannan kira ne yayin da matasan ƙasar suka fara zanga-zangar kokawa kan matsin rayuwa ta kwana goma daga ranar Alhamis.

A tattaunawarsa da BBC, Abbas ya ce ya gana da matasa inda ya ji ƙorafe-ƙorafensu, kuma tuni ya isar da su ga shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu.

Najeriya dai na fama da matsalar tashin farashin kayan masarufi da zubewar darajar kudin ƙasar.

Abubuwa sun ƙara dagulewa ne tun bayan da shugaban ƙasar, Bola Tinubu ya cire tallafin man fetur a watan Maris ɗin 2024.

Gwamnati ta yi ta ƙoƙari wajen ɗaukan matakan lallashi domin hana matasan fara zanga-zangar da suka shirya.

A baya-bayan nan shugaban ƙasar ya amince da sabon albashi mafi ƙanƙanta na naira 70,000.

Haka nan Gwamnatin Tarayya ta ce ta bai wa kowace jiha, har da Abuja tirelolin shinkafa 20 domin raba wa al'umma.

Sai dai duk da haka mutane na cewa suna cikin matsin rayuwa, inda ba kowa ne ke iya cin abinci koda sau biyu ne ba a rana.