Mata su tashi tsaye su nemi ilmi - Matar Shugaban Majalisar Wakilan Najeriya

Bayanan bidiyo, Uwargidan shugaban majalisar wakilai ta shawarci mata su kara zage damtse wajen neman ilmi don su yi fice a rayuwa kamar gwarazan da suka ci Gasar rubuta gajerun labarai ta mata zalla ta BBC Hausa.Hussaina Tajuddeen Abbas, ta kuma karfafa gwiwar mata su rika ba da gudunmawa wajen tafiyar da gidajensu na aure da kuma tallafawa mahaifansu, domin ganin budi a rayuwa.Haka zalika, ita ma uwargidan gwamnan jihar Katsina, Zulaihat Dikko Radda, yayin taron bikin karrama matan da suka yi zarra a gasar Hikayata ta bana ta shawarci mata su kara tashi tsaye a kan duk abin da suka sanya gaba.
Mata su tashi tsaye su nemi ilmi - Matar Shugaban Majalisar Wakilan Najeriya