Yadda ake hada-hadar naman kwaɗo a jihar Jigawa

Bayanan bidiyo, Latsa hoton sama ku kalli bidiyo:
Yadda ake hada-hadar naman kwaɗo a jihar Jigawa

Kasuwar kwaɗi da ke garin Hadeja na jihar Jigawa ta zamar wa masu zuwanta dole saboda a cewarsu sai a nan suke samun abinda suke nema.

Mazauna sassan Najeriya kan je kasuwar don saye ko sarar gasassun kwaɗin, wadda ke ci duk ranar Lahadi a jihar da ke arewa maso yammacin ƙasar.

"Shekarata 12 in wannan sana'ar. Na gina gida na kaina, na yi aure," in ji wani daga cikin 'yan kasuwar.

Ana kai kwaɗin ne daga wurare kamar Nijar da Chadi da Togo da Geidam a jihar Yobe.