Ku San Malamanku tare da Malama Saratu Sheikh Nasiru Kabara

Bayanan bidiyo, Malama Saratu Sheikh Nasiru Kabara
Ku San Malamanku tare da Malama Saratu Sheikh Nasiru Kabara

An haifi Malama Saratu Sheikh Nasiru Kabara a unguwar Kabara da ke tsakiyar birnin Kano a 1968, gidan Ƙadiriyya.

'Ya ce ga babban malamin addinin Musuluncin nan na Kano, Marigayi Sheikh Nasiru Kabara.

Ta shaida wa BBC cewa ta fara karatun allo a gidansu, kafin ta shiga firamaren Ma'ahad Sheikh Nasiru Kabara a birnin Kano, kafin ta samu damar karanta fannin Hadisai da Addinin Musulunci da ke ƙarƙashin Jami'ar Usman Ɗanfodio.

Malama Saratu ta ce ta yi koyarwa a makarantu da dama a Sokoto ciki har da Darul Hadith Islamiyya.

Ta ce ta karanta litattafai kamar Riyadus Salihina da Iziyya a wajen mahaifinta, Sheikh Nasiru Kabara, sannan ta yi karatu a hannun malamai kamar Sheikh Bello Abubakar Kanwa da Farfesa Umar al-jannare lokacin da take Sokoto. Sai kuma Malama Hajiya Amina da Malama Maimuna da Sheikh Bazallahi Nasiru Kabara.

Malama Saratu Nasir Kabara ta ce tana ɗaya daga cikin matan da suka fara buɗe makarantar matan aure a garin Dawakin Kudu cikin jihar Kano.