'Dalilinmu na neman tallafin Majalisar Ɗinkin Duniya don inganta karatun allo'
Wani yunƙuri da Gidauniyar Ɗahiru Bauchi ke yi na inganta karatun allo na shirin sauya yadda ake koyo da koyar da Alƙur'ani mai girma a arewacin Najeriya.
Yunƙurin da gidauniyar ke yi ƙarƙashin jagorancin shehin malamin addini kuma jigo a ɗariƙar Tijjaniyya, Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi, ya kai ta har zuwa Majalisar Ɗinkin Duniya (MMD).
Karatun allo, wanda ake yawan alaƙantawa da almajiranci da kuma yin bara, na cikin abubuwan da mazauna arewacin Najeriya ke yawan muhawara a kai, musamman saboda yadda iyaye ke kai ƙananan yara garuruwa masu nisa domin yin karatun ba tare da kula da ci ko shansu ba.
Wakilai daga gidauniyar na cikin mutanen da suka wakilci Najeriya a babban taron MDD wato UNGA na 2024 da aka gudanar a birnin New York na Amurka daga 24 zuwa 28 na watan Satumban da ya gabata.
Shugaban gudanarwa na gidauniyar, Sheikh Ibrahim Ɗahiru Bauchi, ya shaida wa BBC cewa sun samu ganawa da Mataimakiyar Babban Sakatare Amina Muhammad yayin ziyarar tasu.
'Abin da muka nema daga Majalisar Ɗinkin Duniya'

Asalin hoton, Ɗahiru Bauchi Foundation
Gidauniyar Ɗahiru Bauchi na gudanar da ayyuka da suka shafi addini, da ayyukan jinƙai, da kuma ba da horo wajen inganta rayuwa.
Kazalika, tana gudanar da ɗaruruwan makarantun koyar da Alƙur'ani a Najeriya da wasu ƙasashen Afirka.
"Mun faɗa wa mataimakiyar sakatare janar cewa muna so a taimaka mana; yadda kuke tura kuɗi wajen taimaka wa karatun zamani muna so ku dinga turo mana kuɗi kai-tsaye domin tsara yadda za a yi karatun allo cikin kwanciyar hankali," a cewar Shiekh Ibrahim.
"Idan [yara] suka yi karatun allo kuma daga baya suka koma karatun zamani ka ga an samu riba kenan. Babban abin da muke nema shi ne a gina mana makarantu, da wurin kwanan ɗalibai, da wurin koyar da sana'o'i."
Haka nan, jami'an MDD sun ce suna so tsarin ya shafi duka ƙasashen Afirka.
Babban jigo a ayyukan MDD shi ne bayar da agaji, inda take da hukumomi daban-daban masu kula da ɓangarori, cikinsu har da International Finance Facility for Education (IFFEd) mai tallafa wa ɓangaren ilimi a duniya.
An ƙaddamar da shirin IFFEd ne a watan Satumban 2022 da zimmar samar da kuɗaɗen da za su dinga cike giɓin kasafin kuɗi a ɓangaren ilimin ƙasashe masu ƙarancin samu da masu tasowa - inda a nan ne kashi 80 cikin 100 na yaran da ba su zuwa makaranta a duniya suke.
"Sun ce mana sun amince, amma mun faɗa musu cewa kuɗaɗen nan 'yansiyasa ake bai wa, su kuma 'yansiyasa ba za su ba ka komai ba idan ba ka tare da su," in ji Sheikh Ibrahim.
"Amma idan ya zama [tallafin] kai-tsaye ne zuwa ga mutanen addini babu ruwanka, za ka yi aikinka ne kuma karatu zai yiwu sosai. Yanzu sun ce mu rubuto musu daftari kan buƙatar."
Ya ƙara da cewa an yi musu alƙawarin haɗa su da sauran hukumomi kamar Bankin Duniya da sauransu.
To ko zuwa yaushe za su kammala haɗa daftarin?
"Muna so mu yi ƙoƙari daga yanzu zuwa wata shida mu haɗa abin, saboda yawansa," a cewar malamin addinin.



