Matashin da yajin aikin ASUU ya sa ya fara sana'ar zane-zanen Larabci
Matashin da yajin aikin ASUU ya sa ya fara sana'ar zane-zanen Larabci
Matashi Dahiru Abubakar Sajo ya faɗa wa BBC Hausa cewa ya fara sana'ar zane-zane cikin harshen Larabci bayan fara yajin aiki da malaman jami'a suka yi a Najeriya.
Dahiru ɗalibi ne a aji na biyar a Jami'ar Modibbo Adama da ke Jihar Adamawa. Ya ce ya samu lambar yabo a shekarar 2020 sakamakon zane-zanen da yake yi.
Akwai nasarori sosai kuma ina fatan wannan sana'a za ta kai ni wurare da dama, ba Najeriya kaɗai ba har ma ƙasashen ƙetare," in ji shi.
Ya ƙara da cewa yana fuskantar matsaloli masu yawa a aikin.



