Me dawo da canjin dala ga masu shiga da shinkafa Najeriya yake nufi?

Rice bags

Asalin hoton, Rice Dealership Ass/Facebook

Masana na ci gaba da tsokaci game da matakin Babban Bankin Najeriya na janye takunkumin da ya sanya na daina samar da canjin dalar Amurka ga 'yan kasuwa masu shigar da kayayyaki guda 43 a kasar ciki har da shinkafa da tumatir da sumunti.

Wasu masharhanta sun ce matakin ba ya rasa nasaba da yunkurin gwamnatin Najeriya na farfado da darajar naira da shawo kan hauhawar farashin kayan masarufi.

Haramcin na shekara ta 2015 wanda kuma ya shafi tufafi da kaji, wani bangare ne na manufofin tsohon gwamnan babban bankin kasar, Godwin Emefiele a wani yunkuri na farfado da darajar naira da ke durkushewa a wancan lokaci.

Matakin ya tilasta wa masu shigar da wadannan kaya neman dala a kasuwar canji, abin da ya jefa ta cikin matsi, saboda karancin dala da hauhawar farashi.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa janye haramcin a yanzu, zai faranta ran masharhanta da masu zuba jari, wadanda ke gargadin cewa takunkumin na nuna cewa babban banki ya ci gaba da aiki da wani nau'in takure harkokin zuba jari.

Bankin na CBN dai ya kuma jaddada wani alkawari da sabon gwamnansa Olayemi Cardoso a watan jiya na biyan bashin kudaden waje da suka taru a kan babban bankin kimanin dala biliyan bakwai.

Reuters ya ce kasar mafi girman tattalin arziki a Afirka tana fadi-tashi wajen shawo kan karancin dalar Amurka a kasuwar hukuma, inda hada-hada ke raguwa ba tare da kakkautawa, abin da kuma ya janyo karyewar darajar naira zuwa wani matsayi mafi kaskanci a kan dala.

Sai dai, sanarwar da mai magana da yawun bankin CBN, Isa Abdulmumin ya fitar ta ce "A wani bangare na nauyin da ya rataya a wuyansa don tabbatar da daidaituwar farashi, babban bankin zai bunkasa yawan dalar Amurka a kasuwar canjin kudaden waje ta Najeriya ta hanyar kai dauki lokaci-lokaci".

r

Asalin hoton, CBN

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Tsawon shekaru masana tattalin arziki da masu zuba jari sun yi ta yekuwa don ganin an dage haramcin bayar da canjin dalar Amurka ga masu shigar da wadannan kaya, abin da suka ce ya haifar da bambancin farashi tsakanin kasuwar 'yan canji da kuma kasuwar hada-hadar kudaden kasashen waje.

Matakin dai kuma ya taimaka wajen kallon da ake yi wa Babban Bankin CBN na son iyakance damar zuba jari, lamarin da ya takaita kai-komon harkokin jari a cikin kasar.

Wani mai sharhi kan manufofin gwamnati Muda Yusuf ya fada wa BBC cewa abu ne da ya saba ka'ida ga babban bankin kasa ya rika zabar wanda ya kamata ya samu canjin kudaden waje. Amma dai wannan mataki zai samar da karin fayyace gudanar da harkoki a bayyane da tsuke gibin da ke tsakanin kasuwar 'yan canji da ta hukuma.

A yanzu ana canzar da dalar Amurka ana canzzar da ita a kan naira1,030 ne a kasuwar canji.

Shi ma Dr Muhammad Shamsuddeen na Jami'ar Bayero Kano ya ce labari ne mafi daɗi cewa, CBN ya ce zai riƙa samar da dala a kasuwa musayar kuɗi a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso.

Shin za a ci gaba da shigo da shinkafa ne?

r

Asalin hoton, Google

Masana da dama na cewa matakin tamkar wata manuniya ce cewa 'yan kasuwa za su samun dalar Amurka cikin farashin hukuma, idan sun cika ka'idojin babban bankin wajen zuwa su sayo shinkafa a kasashe kamar Thailand da Brazil da Indiya, don shigar da ita Najeriya.

Najeriya dai ta sanya haramcin shigar da shinkafa ta kan iyakokin kasa daga waje a 2016.

"Maganar shinkafa ta fi ɗaukar hankali, kuma gaskiyar magana kowa zai yi farin ciki da ita.

Ya ce ana iya fahimtar matakin samar da dalar ga masu shigar da kaya 43 ciki har da shinkafa, a matsayin janye haramcin shiga da kayan Najeriya. "Domin in dai an ce a hukumance, za a ba ka kudin kasar waje domin siyo wani kaya, to wannan yana nuna cewa a hukumance, an yarda ka shigo da wannan kayan", cewar Shamsuddeen.

"Abin da ya kamata a sake neman fashin baƙi a kai shi ne, ko jami'an kwastam sun san da wannan mataki? Wacce irin sanarwa su aka ba su a hukumance?"

Sai dai wasu masana kamar Aliyu Da'u wani tsohon ma'aikacin banki na ganin matakin a matsayin mayar da hannun agogo baya ga 'yan Najeriya.

"Mutane da dama sun fara sabawa, kuma an yi wannan shiri domin taimakawa masu sarrafa kaya a cikin gida kamar manoman shinkafa da masu samar da sumunti, kuma duka suna ƙoƙari.

"Duk ƙoƙarin da waɗannan mutane suka yi a baya zai tashi a kawai," in ji Aliyu Da'u.

'Tufka da warwara'

Sai dai masanan sun ce a wani bangare sanarwar CBN, yana cin karo da juna.

"Babu yadda za a yi, ka ce kasuwa za ta yi wa abu farashi, amma kai za ka dinga fadar farashin", in ji Dr Muhammad Shamsuddeen.

A cewarsa, akwai cin karo da juna a sanarwar CBN, inda ya ce ga mai son sanin farashin dalar Amurka ya je ya duba shafinsa na intanet. Masanin ya ce inda kaya yake a can ya kamata a samu farashi, amma ba a wajen hukuma ba.

"Yawan dalar a kasuwa, shi ne zai nuna farashinta."