Argentina ta je Qatar bayan wasa 35 a jere ba a doke ta ba

Asalin hoton, Getty Images
Argentina za ta buga Gasar Kofin Duniya a Qatar karo na 18 daga 22 da a gudanar tun fara wasannin a 1930.
Argentina tana rukuni na uku da ya hada da Saudi Arabia da Poland da kuma Mexico.
Za a fara Gasar tsakanin 20 ga watan Nuwamba zuwa 18 ga watan Disamba.
Sai dai wannan karon Argentina karkashin kyaftin Lionel Messi za ta shiga wasannin Qatar, bayan karawa 35 a jere ba tare da an doke ta ba.
Ta fara wannan bajintar daga ranar 6 ga watan Yulin 2019, bayan doke Chile 2-1 a Copa America a Brazil.
Cikin kwazon da ya kai ta samun tikitin shiga Gasar Kofin Duniya a Qatar har da lashe Copa Ameria da cin wasa 24 da canjaras 11.
Wasa na 35 a jere da ba a doke ta ba shi ne wanda ta ci Jamaica 3-0 a karawar sada zumunta ranar 27 ga watan Satumba.
Argentina mai kofin duniya biyu ta yi ta uku a Gasar karo uku a 1930 da 1990 da kuma a 2014.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Haka kuma jumulla Argentina ta yi nasara a wasa 47 daga 81 a dukkan karawar Gasar Kofin Duniya a tarihi.
Jerin wasa 35 da Argentina ta yi a jere ba a doke ta ba
Lamba Rana. Sakamako Gasa
1 July 6, 2019 Argentina 2-1 Chile Copa America
3 Sept. 10, 2019 Argentina 4-0 México Friendly
4 Oct. 9, 2019 Germany 2-2 Argentina Friendly
5 Oct. 13, 2019 Argentina 6-1 Ecuador Friendly
6 Nov. 15, 2019 Argentina 1-0 Brazil Friendly
7 Nov. 18, 2019 Argentina 2-2 Uruguay Friendly
8 Oct 8, 2020 Argentina 1-0 Ecuador World Cup Qualifier
9 Oct. 13, 2020 Bolivia 1-2 Argentina World Cup Qualifier
10 Nov 12, 2020 Argentina 1-1 Paraguay World Cup Qualifier
11 Nov. 17, 2020 Peru 0-2 Argentina World Cup Qualifier
12 June 3, 2021 Argentina 1-1 Chile World Cup Qualifier
13 June 8, 2021 Colombia 2-2 Argentina World Cup Qualifier
14 June 14, 2021 Argentina 1-1 Chile Copa America
15 June 18, 2021 Argentina 1-0 Uruguay Copa America
16 June 21, 2021 Argentina 1-0 Paraguay Copa America
17 June 28, 2021 Argentina 4-1 Bolivia Copa America
18 July 3, 2021 Argentina 3-0 Ecuador Copa America
19 July 6, 2021 Argentina 1-1 (3-2) Colombia Copa America
20 July 10, 2021 Brazil 0-1 Argentina Copa America
21 Sept. 2, 2021 Venezuela 1-3 Argentina World Cup Qualifier
22 Sept. 9, 2021 Argentina 3-0 Bolivia World Cup Qualifier
23 Oct. 7, 2021 Paraguay 0-0 Argentina World Cup Qualifier
24 Oct. 10, 2021 Argentina 3-0 Uruguay World Cup Qualifier
25 Oct. 14, 2021 Argentina 1-0 Peru World Cup Qualifier
26 Nov. 12, 2021 Uruguay 0-1 Argentina World Cup Qualifier
27 Nov. 16, 2021 Argentina 0-0 Brazil World Cup Qualifier
28 Jan. 27, 2022 Chile 1-2 Argentina World Cup Qualifier
29 Feb. 1, 2022 Argentina 1-0 Colombia World Cup Qualifier
30 March 25, 2022 Argentina 3-0 Venezuela World Cup Qualifier
31 March 29, 2022 Ecuador 1-1 Argentina World Cup Qualifier
32 June 1, 2022 Italy 0-3 Argentina Finalissima
33 June 5, 2022 Argentina 5-0 Estonia Friendly
34 Sept. 23, 2022 Argentina 3-0 Honduras Friendly
35 Sept. 27, 2022. Argentina 3-0 Jamaica Friendly
'Yan wasan da Argentina ta je da su Qatar:

Asalin hoton, Getty Images
Masu tsaron raga: Emiliano Martinez (Aston Villa), Franco Armani (River Plate) and Geronimo Rulli (Villarreal)
Masu tsaron baya: Gonzalo Montiel (Sevilla), Nahuel Molina (Atletico Madrid), German Pezzella (Real Betis), Cristian Romero (Tottenham Hotspur), Nicolas Otamendi (Benfica), Lisandro Martinez (Manchester United), Juan Foyth (Villarreal), Nicolas Tagliafico (Olympique Lyonnais), Marcos Acuna (Sevilla)
Masu buga tsakiya: Leandro Paredes (Juventus), Guido Rodriguez (Real Betis), Enzo Fernandez (Benfica), Rodrigo De Paul (Atletico Madrid), Exequiel Palacios (Bayer Leverkusen), Alejandro Gomez (Sevilla), Alexis Mac Allister (Brighton & Hove Albion)
Masu cin kwallaye: Paulo Dybala (AS Roma), Lionel Messi (Paris St Germain), Angel Di Maria (Juventus), Nicolas Gonzalez (Fiorentina), Joaquin Correa (Inter Milan), Lautaro Martinez (Inter Milan), Julian Alvarez (Manchester City).











